Gwamnan Jihar Oyo Ya Bada Umarnin Komawa Manyan Makarantu a Jihar

0
125

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bada umarnin dawowa karatu a manyan makarantu mallakar jihar .

Mista Makinde ya bayar da umarnin ne jiya Talata a wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar, Olasukanmi Olaleye ya fitar.

Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da ranar 28 ga watan Satumba a matsayin ranar komawa makaranta a manyan makarantun jihar.

Sanarwar komawa makarantun na zuwa ne duk da gargadin da kungiyar malaman jami’i’o ta ASUU da ta malaman makarantun Fasaha(ASUP) su ka yi na cewa lokacin bude manyan makarantu bai yi ba saboda Cutar COVID-19.

Mista Makinde ya kuma amince da sabuwar Kalandar Karatu ga makarantun Firamare da Sakandire a jihar.

“Ranar komawa makaranta ta kakar karatu ta shekarar 2020/2021 ga makarantun gwammati da masu zaman kan su kamar yadda ma’aikatar ilimi ta sanar zai fara ne daga ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2020″.

” Makarantu za su dinga karatu da safe da yammaci, yan aji 1 zuwa aji na 3 na makarantun Piramare za su dinga karatu daga karfe 8 na safe zuwa 11 na safe, yan aji 4 zuwa na 6 za su dinga karatu daga 12 na rana zuwa 3 na yamma”.

“Dole dukkan makarantu su samar da kwamitin kar ta kwana kan yaki da COVID-19, wanda zai samu shugabancin shugaban makaranta da sauran ma’aikata guda biyu”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here