‘Da Amincewar Iyayena na Shiga Harkar Film’ -Isah Jibril

0
678

Mai Bada Umarni a shirin film na masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Isah Jibril Lawal ya ce da amincewar iyayen sa ya fara harkar fina-finai, sannan tun yana karamin yaro yake sha’awar shiga shirin Filma.

Isah Jibril , wanda shine ya bada umarni a shirin Film din ‘Rabin Jiki’ ya bayyana hakanne yayin tattaunawa da jaridar PRIME TIME NEWS a daren jiya Talata a Kano.

“Na tsinci kaina, a harkar film a shekarar 2011-2012, amma kafin nan, sanda ina yaro na kasance da yawan son kwaikwaye-kwaikwaye, idan na kalli film sai nace nine wane nine wane, musamman idan naga jarumi sai na ce sai na kwaikwaya, sannan kuma na taba harkar waka wacce ita ta kaini masana’antar shirya fina-finai”.

Mai bada umarnin ya ce lokacin da zai fara aiki da kamfanin AUAB sai da aka ce ya kawo wanda zai tsaya masa in da ya ce yaje ya fadawa mahaifan sa.

“A lokacin aka ce sai na kawo wanda zai tsaya min na cewa ya amince nayi harkar Film, na zo na sami mamana na samu mahaifina nayi mu su magana, suka ce toh ba laifi, Allah Ubangiji ya zaba abinda yafi Alkhairi, muna ma fatan Alkhairi, mu dai abinda muke so duk inda kaje ka tsinci kanka ka kasance mai tsoron Allah, mai kare kanka, mutuncinka addinin ka”.

Isha Jibril ya kuma yi bayanin yadda ya tsinci kan sa a matsayin mai bada Umarni a shirin Film.
“Na tsinci kai na, a mai bada umarni a shirin Film Saboda a kamfanin da nake aiki a da, AUAB Film Production da dadewa irin mu je muna taro ba aiki mun dau tsawon shekaru uku ko hudu ba tare mun fita mun yi aiki ba kuma duk satin duniya za’a ce mu zo taro, toh idan aka zo sai a shiga fannin Reharsal, wani lokacin shi mai gidan mu idan bai zo ba, zai iya cewa mu fara wani abun da yakawo mu, toh idan muna yi tunda daga nan sai naga tun da baya nan kuma ya wakilta a dinga bayar da umarni, toh ana cikin hakan sai naga ay indai bada umarni ne toh Allah ya hore min.

“Idan ana aiki sai naje na duba naga yadda Director yake aikin sa”.

Mai bada Umarnin ya ce ya fuskanci kalubale yayin da ya ce ya fi son zama Mai bada umarni akan zama Jarumi, sannan ya samu nasarori da dama ciki kuwa har da shirin ‘Rabin Jiki’.

Shima ana sa bangaren mashiryin shirin na ‘Rabin Jiki’, Saminu Uba Mai Turare ya ce, Labarin shirin ‘Rabin Jiki’ ya kunshi soyayya, Fadakarwa da Ban dariya.

Sannnan ya ce shirin zai dinga fitowa ne a Series duk ranar Juma’a a You Tube Channel din su mai suna ‘Rabin Jiki’.

Sannnan suna fitar da Film din ne karkashin Kamfanin su mai suna, Yamadawa Film Production.

Daga Karshe ya yiwa masoyan su fatan Alkhairi tare da yin kira gare su da su tuntube su kan dukkan abinda ba su gane ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here