Osinbajo Na Halartar Taron ECOWAS a Kasar Ghana

0
87

Mataimakin shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bar birnin tarayya Abuja,  a safiyar yau zuwa birnin Accra na Ghana don halartar taron kungiyar raya tattalin azrkin kasashen yammacin Africa(ECOWAS) na musamman kan rikicin kasar Mali.

A wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin shugaban kasar kan kafafen yada labarai, Laolu Akande ya fitar, ta ce Osinbajo wanda ke wakiltar shugaban Kasa Buhari a wajen taron, zai hadu da sauran shugabannin yammacin Afrika don tattauna rikicin siyasar Kasar Mali da fannin tsaro a yankin gabadaya.

Taron na Birin Accra, zai samar da wasu bangarori na kokarin shugabannin yankin wajen kawo karshen matsalar rikicin siyasar kasar.

Sanarwa ta kara da cewa, mataimakin shugaban kasar zai yi amfani da ziyarar wajen haduwa da wakilan yan Najeriya mazauna kasar ta Ghana don tattauna irin matsalolin da suke fuskanta.

Mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar karamin ministan harkokin wajen kasarnan, Amb. Zubairu Dada.

Kuma ana sa ran Osinbajo zai dawo Abuja a yau bayan kammala taron a kasar Ghana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here