
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto mutane goma da suka makale a wani gini da ya fado a unguwar Gwammaja ‘Yan Kosai dake karamar hukumar Dala ta jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar, Saidu Muhammed, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa yau Talata, a Kano.
“Mun karbi kira da misalin karfe 1:30 na dare a ranar Talata daga wani mutum mai suna Abdullahi Muhammad.
” Bayan samun bayanin, mun yi sauri wajen tura tawagar ceto zuwa wajen da abun ya faru da misalin karfe 1:37 na dare.
“Mun gano cewa gidan mai hawa daya, ya rushe akan mutane 10 mazauna gidan sannan bulo da kasa sun danne mutanen”, Inji Malam Muhammad.
Ya ce mutane 8 daga cikin su an ceto su a raye sannan an kai su zuwa Asibitin Murtala Muhammad dake Kano.
Ragowar mutane biyu kima sun rasa ran su yayi n da aka kai gawar su asibiti in da aka tabbatar da mutuwar ta su.
Ya shawarci mazauna jihar da su kula da muhallin su tare da kaucewa zama a gidajen da suka lalace.