Muna Ciyo Bashi ne Don Jawo Hankalin Masu Zuba Hannun Jari -Buhari

0
114

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanin cewa dalilin da ya sa gwamnatin sa ta ke ciyo bashi shine don samar da tsare-tsare da ayyuka da za su janyo hankalin masu zuba jari.

A wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasar kan fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, ta ce, Buhari ya yi bayanin ne a yau Talata yayin tattaunawa tare da kwamitin bada shawara na fadar shugaban kasa kan tattalin arziki.

In da ya ce Najeriya dole ne ta gyara tituna don ceto rayuka daga fadawa hadarurruka a kan hanya.

“Muna da kalubale da yawa a fannin ayyuka da tsare-tsare. Mun karbi bashi don yin ayyuka tituna, titin jirgin kasa da wuta, wanda hakan zai jawo hankalin masu zuba hannun jari su zo nan su zuba kudin su”, Inji Shugaban kasar bayan ya saurari jawabi daga kwamitin wanda Farfesa Ayo Salami ke jagoranta.

Buhari ya yi bayanin matsayin harkar noma a shirin gwamnati na rage zaman kashe wando da talauci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here