Mun Raba Tallafin Corona Miliyan Dubu 69 Ga Magidanta da Yan Kasuwa Dubu 140 -CBN

0
117

Babban Bankin Najeriya(CBN), ya ce ya raba tallafin kudi Miliyan dubu 69 daga cikin Miliyan dubu 100 da ya ware a matsayin tallafin COVID-19 ga kananan yan kasuwa da magidanta.

Gwamnan babban bankin na Najeriya, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a yau Talata yayin bude taron Charted Institute of Bankers of Nigeria(CIBN), a Abuja.

Idan za’a iya tunawa dai, yayin dokar kulle ta COVID-19, Babban Bankin ya sanar da ware Biliyan 50 don bayar da tallafi ga kananan yan kasuwa da magidanta.

Kudin an raba su ne ta hanyar Bankin NIRSAL.

Yayin da karin bayani kan shirye-shiryen bayar da tallafi da Bankin na CBN ke yi, Emeifele ya ce Yan Najeriya sun yi farin ciki bisa kirkirar shirin tallafawa kananan yan kasuwa da magidanta wanda aka ware Biliyan 100.

“Da farko mun shirya raba Naira Biliyan 50. Kamar yadda muka gani magidanta na bukatar kari saboda illar da annobar ta yi mu su, CBN ya yanke shawarar kara yawan kudin tallafin daga Miliyan dubu 50 zuwa Miliyan dubu 100. Sannan zuwa yau an raba Biliyan 69 ga magidanta dubu 140 da yan kasuwa”, inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here