Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano Ta Mika Miyagun Kwayoyin da ta Kama ga Hukumar NDLEA

0
107

Kwamitin kar ta kwana na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Kano ya kama muggan kwayoyi da ake zargin har da tabar wiwi da nauyin su ya kai Kilo Gram 53.8.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar, Hadiza Mustapha Namadi wacce ta aikowa jaridar PRIME TIME NEWS a yau Talata.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Aminu Tsanyawa ya ce kwamitin kar ta kwanan ya kuma kama jabun magunguna wanda aka so raba su a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ya samu wakilcin shugaban kwamitin kar ta kwanan, Phaemacist Ghali Sule yayin mika miyagun kwayoyin da aka kama ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA.

Yayin da yake karbar kwayoyin, Kwamandan hukumar NDLEA na Kano, Dr. Ibrahim Abdul, ya godewa ma’aikatar lafiya bisa goyan baya da hadin kai da take ba wa hukumar.

Dr. Ibrahim ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe wajen kawar da matsala sha da fataucin miyagun kwayoyi la’akari da samun yan Najeriya dake fadawa cikin matsalar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here