Ganduje Ya yabawa Kokarin Ize-Iyamu a Muhawarar ‘Yan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Edo

0
128

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya yabawa kokarin dan takarar Gwamna na jami’iyyar APC a jihar Edo, Pastor Ize-Iyamu a muhawarar da aka gudanar tsakanin yan takarar gwamnan da gidan Talabijin na Channel ya shirya.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya ce Ize-Iyamu ya doke, Gwamna Godwin Obaseki dan takarar jami’iyyar PDP yayin muhawarar da aka yi ranar Lahadi.

Ganduje, Wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zaben jami’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo ya ce, “a dukkan fannonin da aka tattauna yayin muhawarar, ya bayyana ga kowa cewa jami’iyyar mu ta APC t shirya ciyar da jihar Edo gaba.

“Shirye-shiryen mu a bangaren tsaro, Ilimi, Lafiya da sauran bangarori ya nuna cewa jami’iyyar mu ta himmatu wajen samar da kyakkwar rayuwa ga jama’a”, inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here