An yi Garkuwa da Tsohon Sojan Kasar Amurka A Jihar Ekiti

0
137

‘Yan Sanda a jihar Ekiti a yau Talata sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun kashe mutum daya tare da sace tsohon sojan Amurka, Maj.Jide Ijadare da wani mutum daya.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar, Sunday Abutu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce abun ya faru ne a Ijan Ekiti, karamar hukumar Gbonyin dake jihar.

“Muna tabbatar mu ku cewa an yi garkuwa da tsohon sojan kasar Amurka da wani mutum daya da misalin karfe 2 na rana a yau Talata.

“Mutum daya ya rasa ran sa yayin kai harin a wata masana’ata dake Ijan Ekiti inda aka yi garkuwa da mutanen biyu.

“Kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’an yanda zuwa wajen sannan muna bibiyar dazukan da suka buya.

“Yan sanda na aiki tare da mafarauta don tabbatar da an kama masu garkuwa da mutanen kuma an gurfanar da su gaban kotu”, Inji Kakakin yan sandan.

Lamarin ya faru ne awanni 24 bayan rahotannin dake cewa an hallaka daraktan mulki na ma’aikatar kananan hukomomin jihar, Mista David Jejelowo, a gidan sa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here