An Chanzar da Dalar Amuruka Daya a Naira 460 a Kasuwannin Bayan Fage

0
123

Darajar kudin Naira a yau Litinin ta fadi da kaso 1.09 yayin da ake chanzar da Dalar Amuruka daya kan Naira 460 a kasuwar bayan fage.

Faduwar Darajar Naira din ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa Buhari ya yi ga babban bankin Najeriya(CBN) kan dakatar da siyar da Dala ga masu shigo da abinci da takin zamani.

A hukumance dai ana chanzar da Kudin Naira a kan 381 a matsayin Dala daya.

A ranar Alhamis ne dai Buhari ya bawa Bankin CBN umarnin dakatar da chanzar da kudaden ketare ga masu shigo da kayan abinci.

Najeriya dai na fuskantar matsalar tattalin Arziki ne bayan karyewar farashin danyen man fetir a kasuwannin duniya wanda annobar COVID-19 ta haifar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here