Zaben Jihar Edo: An Tura Jami’an ‘Yan Sanda 31, 000 Jihar

0
140

Babban Sufeto Janar na Yan sanda na kasa, Mohammed Adamu a yau Litinin ya bayyana cewa kimanin jami’an ‘yan sanda dubu 30 da 1 aka tura jihar Edo.

Adamu, ya bayyana hakanne yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta shirya a garin Benin a dai-dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar ranar 19 ga watan Satumba.

Sannan ya yi bayanin cewa, rundunar za ta ci gaba da kasancewa ba mai nuna fifiko ga wani bangare ba kuma ta himmatu wajen ganin anyi sahihin zabe a jihar.

Ya ce, tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki na daga cikin damar haduwa da yan siyasar jihar don ganin anyi zabe lafiya.

Ya kara da cewa, jami’an da aka tura jihar za su tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’umma a fadin shiyyoyi uku na jihar da mazabu 192 da kuma runfunan zabe 2, 000 a jihar.

Sannan ya shawarci iyaye su gargadi ya’yan su wajen kaucewa shiga rikici.

Sannan ya yi kira ga al’umma su bayar da hadin kai don ganin anyi zabe lafiya a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here