Za’a dinga Ba wa Mata Dubu 2 Tallafin Kudi Naira Dubu 20 Duk Wata a Jihar Zamfara

0
134

Hajiya Balkisu Matawalle, matar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ta tabbatar wa da mata a jihar cewa mata dubu biyu za su dinga karbar kudi Naira dubu 20 duk wata don bunkasa rayuwar su ta yau da kullum.

Ta bayar da tabbacin ne yayin da ta ke karbar dubban mata wadanda suka koma jami’iyyar PDP daga APC, a garin Gusau jiya Lahadi.

Ta ce, gwamnatin jiha ta samar da shirin samarwar da mata aikin yi don bunkasa rayuwar mata a jihar in da ta kara da cewa mata 1, 800 yanzu haka suna cin gajiyar shirin.

“A karkashin wannan shirin, adadin mata 1, 800 su na karbar kudi dubu 20 duk wata.

“Muna duba yuwuwar fadada yawan masu amfana da shirin zuwa dubu biyu”, Inji ta.

Hajiya Balkisu Matawalle ta godewa matan bisa shiga jami’iyyar PDP don ciyar da jihar gaba.

” Na yabawa matakin da kuka dauka na shiga PDP. Na yi muku Alkawarin cewa za’a dauke matsayi daya da duk wani dan PDP.

“Wannan gwamnati karkashin jami’iyyar PDP, kofar mu a bude ta ke ga dukkam kungiya ko dai-dai kun mutane don ciyar da jihar nan gaba.

” Ina shawartar mutanen jiharnan su yi watsi da duk wata tsangwama wajen bayar da goyan baya ga gwamna Matawalle don aiwatar da nagartattun manufofi da ayyuka masu amfani a jihar nan, ” inji ta.

Hajiya Hadiza Ba’ara, wacce ta yi magana a madadin matan, ta ce sun yanke shawarar shiga jami’iyyar PDP ne bayan samar da zaman lafiya da gwammatin Matawalle ta yi a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here