Yan Najeriya na Shan Bakar Wahala, Sakon Jega Zuwa ga Buhari

0
251

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Attahiru Jege; da tsohon Archbishop na majami’ar Abuja, Cardinal John Onaiyeka , sun fadawa shugaban Kasa Buhafi cewa yan Najeriya na shan jar wuya har kala biyu, ta rashin tsaro da kuma wacce annobar COVID-19 ta haifar.

Sun kuma yi kira ga shugaban kasar ya yi duk mai yuwuwa wajen kawo karshen matsalar tsaro ko da kuwa ta hanyar korar manyan hafsoshin tsaron kasarnan ne.

Sun bayyana hakanne a wata sanarwa da suka fitar jiya Lahadi mai taken ‘Shugaban Kasa, Gwamnoni: Lokacin zaman lafiya yayi’.

Sanarwa tana dauke da sa hannun Jega, Onaiyekan, Janar Martin Agwai, Amb. Fatima Balla, Farfesa Jibril Ibrahim, Misis Aisha Muhammad Oyebode, Dr. Nguyan Feese, Dr. Usaman Bugaje da Dr. Chiris Kwaja wadanda dukkan su mambobi ne na kungiyar Nigeria Working Group on Peace Building and Governance.

Sanarwar ta ce “Kasar Najeriya kamar sauran kasashen duniya ta na yaki da annobar Corona. Haka kuma yan kasa na shan wuya iri biyu saboda suna fama da matsalar tsaro da rikice-rikice a fadin kasar nan.

” Gwamnatin tarayya dole ne ta kawo gyara a matsalar tsaro da ake fuakanta a fannin tsaro idan tana son samun nasara a yaki da annoba”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here