Shin Zaben Jihar Edo zai zama Irin Zaben gwamnan jihar Kano na 2 ne

0
423

Wata majiya ta shaidawa jaridar Sahara Reporters cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa(INEC), ta tura Arab Shehu zuwa jihar Edo duk da zargin bayanan dake nuna cewa ya yi murdiya a zaben gwamnan jihar Kano na shekarar 2019.

Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, ya amince da tura kwamishinonin zabe biyar zuwa jihar ta Edo yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 19 ga watan Satumba.

Kwamishinonin zaben da aka tura sun hada da; Kwamishinan hukumar zabe na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu, wanda ake gani ya gudanar da zabe mafi rikici da kalubale a tarihin Najeriya.

Sannan ya kara shiga zaben jihar Kogi wanda aka yi shi ranar 16 ga watan Nuwamba.

Idan za’a iya tunawa dai, Zaben gwamnan jihar Kano na shekarar 2019 wanda Arab Shehu ya jagoranta ya faru ne cikin rikici inda ake zargin mutane 10 sun rasa ran su.

Kwanaki kadan kafin zaben na jihar Kano, wani faifan bidiyo da ke nuna shugaban jami’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana zaben a matsayin “Ko da tsiya – tsiya”.

Duk da samun rahotannin rikici a zaben, Arab shehu ya sanar da dan takarar jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ganduje ya sha kashi a zaben farko na 9 ga watan Maris da tazarar kuri’a 26, 000 amma zaben zagaye na biyu ya yiwa dan takarar jami’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusif shal.

A zaben dai na jihar Kano, yan daba sun kai hari ga yan jaridu wanda hakan ya hana su gudanar da aikin su.

Gwamman jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje dai shine zai jagoranci tawagar jami’iyyar APC a zaben na ranar Asabar mai zuwa tare da dafawar gwamman jihar Imo.

Shima tsohon gwamnan jihar Kano kuma babban mai hamayya da Ganduje, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso an hango shi cikin wani faifan Bidiyo inda yake jawabi ga magoya bayan jami’iyyar yan asalin Arewa dake zaune a jihar ta Edo inda ya bukace su,  su zabi Godwin Obaseki na PDP kuma su tabbata sun tsare kuri’un su don gudun ‘kar a mai-mai ta abin da ya faru a Kano’.

Wasu dai na ganin manyan jagororin siyasar Kano suna amfani da zaben na jihar Edo wajen gwada kwanjin su da karfin fada a ji a siyasar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here