Kashi 98 na Malaman Makaranta a Jihar Kaduna Basu san me ne ‘Dyslexia’ Ba – Cibiya

0
152

Cibiyar kula da cutar rashin gane karatu da iya furta kalma ta Amina Dyslexia, Kaduna ta bayyana matukar damuwa bisa karancin fahimtar cutar tsakananin malaman makaranta a jihar Kaduna, inda ta bayyana cewa kashi 98 na malaman ba su san illar cutar ba wacce ke sanya yara wahala wajen yin karatu ko rubutu.

Anita Kevin, Darakta a cibiyar ta Amina Dyslexia ce ta bayyana hakanne yayin tattaunawa da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN a Kaduna.

Misis Kevin ta yi bayanin cewa yanayin ya na sanya wahala ga kwakwalwa wajen samun bayanai, inda ta kara da cewa babbar alamar cutar ta Dyslexia shine shan wuya wajen hada kalmomi yayin furtasu.

Misis Kevin ta yi bayanin cewa cutar ta shafi yadda kwakwalwa ta ke samun bayanai da kuma furta kalmomi, wanda hakan yake shafar gane kalma, hada jumla da hada kalmomi wajen furta su.

Misis Kevin ta ce, yanayin, idan bai samu hanyar koyarwa da ta dace ba da bayar da horo zai iya haifar da matsala, da fushi.

Daraktan ta ce cutar ta Dyslexia ita ce ke da alhakin samun kashi 85 na manyan mutane da ba su yi karatu ba, yayin da ake samun yaro daya a duk cikin yara 5 dake fuskantar barazanar barin makaranta daga cutar ta Dyslexia.

Ta ce binciken da cibiyar ta gudanar a kwanakin nan ya nuna cewa kashi 98 na malaman makaranta a jihar Kaduna ba su taba jin kalmar ba kuma ba su san illar ta kan sha’anin koyarwa ba.

Ta kara da cewa rashin sanin yanayin cutar ya fara daga malaman makaranta har zuwa masu makarantun, da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki na fannin ilimi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here