Bamu Shirya Bude Iyakokin Kasarnan a Yanzu ba -Buhari

0
153

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a karshen makon nan ya ce, gwamnatin sa ba ta shirya bude iyakokin kasarnan a yanzu ba, inda ya bukaci yan Najeriya su yi amfani da abinda ake samarwa a gida.

Yayin da yake amsa tambayar manema labarai a filin sauka da tashin jirage na Sir Ahmadu Bello dake Birin Kebbi yayin ziyarar duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar ta Kebbi, Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Ministan Noma, Sabo Nanono, ya ce gwamnatin tarayya ta shirya bayar da tallafi ga manoma don bunkasa samar da abinci a gida watakil ma har a fitar da shi waje.

Ya yi bayanin cewa, Shinkafar da ake samarwa a jihohin Niger, Taraba, Jigawa da Kebbi kadai za ta iya ciyar da Najeriya inda ya ce “Me yasa ake shigo da abinci yayin da zamu iya samar da su”?.

Ministan ya kara da cewa, Shugaban kasa ne ya turo ni don nazo naga irin asarar da aka yi a jihar Kebbi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here