‘Yan Sanda a Kano Sun Kama Wani Dan Kasuwa Bisa Zargin Karkatar da Tallafin rage Radadin Corona

0
377

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta kama wani dan kasuwa mai shekaru 30, mai suna Yusif Abdullahi , bisa zargin karkatar da taliyar tallafin rage radadin Corona da kudin ta ya kai Miliyan 4, 111, 800 da gamayyar kungiyoyin yaki da annobar COVID-19 suka bayar.

Yayin da yake holan wanda ake zargin tare da wasu mutane sama da 200 da ake zargin su da aikata laifuka daban-daban a shelkwatar hukumar dake Bombai a Kano, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Habu Sani, ya ce wanda ake zargin ya karkatar da Carton 1, 950 na taliyar yan yara wacce za’a raba ta a jihar Benue.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce “Taliyar da aka gano a wajen wanda ake zargin an rubuta karara a jikinta cewa ‘ba ta siyarwa ba ce’.

“Jami’an mu sun kama mutumin bayan samun bayanai kan hannu da yake aciki kan badakalar”.

Sannan ya ce, taliyar da aka samu a wajen dan kasuwar wanda ke siyar da kayan abinci a kasuwar Singer na daga cikin Carton 3850 da aka karkatar kuma aka siyar.

Yayin da yake magana da ‘yan Jarida, Dan Kasuwar Yusif Abdullahi ya tabbatar da cewa an samu taliyar a wajen sa.

Ya yi bayanin cewa ya samu taliyar ne daga wasu da suka amfana da talllafin kuma suka chanza taliyar da wasu kayan abincin daban.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here