Shiryawa Matakan Kariya da Kula da Cutukan da ake dauka ta Jiki Ya zama Dole – GSA

0
102

A yayin da ake bikin ranar cutar da ake dauka ta jiki ta duniya a duk ranar 13 ga watan Satumba na kowacce shekara, Kungiyar Global Sepisis Alliance ta tunatarwa gwamnatoci, mahukunta masu kula da fannin lafiya, kwararru da masu ruwa da tsaki cewa cutukan da ake dauka ta jiki dole a dauke su a matsayin annobar duniya da za’a yi maganin ta.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce Annobar COVID-19 ta yi nuni da cewa, cutukan da ake iya dauka ko ana yada su ko ba’a yada su, sun ci gaba da zama barazana ga duniya, sannan kariya da maganin cutukan da ake dauka ta  jiki yana daga cikin bangarorin shawo kan matsalar.

“Bikin Ranar cutukan da ake dauka ta jiki ta shekarar 2020 tazo ne a dai-dai lokacin da mutane ke fuskantar babbar annoba a wannan lokacin cewar shugaban GSA, Farfesa Konrad Reinhart, “wadanda suka kamu da cutar COVID-19 da wadanda suka harbu da cutur mutuwar jiki daga abin da ba’a iya ganewa na kwayoyin cuta Kamar kwayoyin bacteria da sauran kwayoyin cuta, Fungi ko Parasites suna daga cikin kwayoyin da ba’a iya ganewa a wajen yin magani.

A farkon wata 6 na fara annobar, mutane miliyan 17.3 ne aka tabbatar sun kamu da cutar sannan mutane 673, 833 ne suka rasu kamar yadda cibiyar kula da cutar ta jami’ar John Hopkins ta bayyana.

Har’ila yau a farkon watanni 6 na shekarar 2017 an samu mutane  miliyan 25 da suka kamu da cutukan da ake dauka ta jiki wanda ya haifar da mutuwar mutane miliyan 5.5 kamar yadda aka rawaito a rahoton bincike da aka wallafa a mujjalar The Lancet2.

Itama ana ta bangaren, mataimakiyar babban darakta na African Sepsis Alliance(ASA) kuma babbar jami’a ta Sepsis Research Group (SIDOK), ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Hajiya Halima Salisu Kabara(RN, MPA, PhD, FWACN) ta ce, akwai bukatar a kara himma wajen fadakarwa, kula da lafiyar majinyata da iyalai wadanda akwai bukatar su shiga a dama da su wajen yakar cutur mutuwar jiki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here