Sai Sabuwar Shekara Daliban Dake Mataki na 1 za su Koma Makaranta a Jihar Legas – LASU

0
138

Daliban shekarar farko na Jami’ar jihar Legas(LASU) zasu jira har 11 ga watan Janairu na shekarar 2021 don dawowa makaranta.

Kafin zuwan lokacin, zasu cigaba da karatu ta kafar sadarwa kamar yadda jami’ar ta bayyana a jiya juma’a.

Wadanda zasu koma makaranta a ranar Litinin sune yan ajin mataki na 4 da mataki na 5 da na 6 sannan za su dinga karatu daga karfe 9 zuwa 3 na yamma cikin ranakun mako.

Masu karatun digirin-digir da na PHD suma za su dawo a ranar Litinin amma za su dinga karatu a ranakun karshen mako kadai.

Sauran yan mataki na 2 zuwa na 5 za su dawo karatu a watan Nuwamba; yayin da yan Part time da yan diploma za su koma karatu a ranar 13 ga watan Nuwamba a ranakun karshen mako.

Jami’ar ta nemi malaman makarantar su tabbatar an sanya safar rufe hanci da baki da kuma tabbatar da yanayi mai kyau a ajujuwa.

Hukumomin jami’ar sun ce matakan an dauke su ne don hana yaduwar annobar Corona.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here