Mu Za mu Lashe Zaben Jihar Ondo -PDP

0
147

Kwanaki 28 kafin zaben gwamnan jihar Ondo, Jami’iyyar PDP ta kaddamar da fara yakin neman zabenta a Akure babban Birnin Jihar a yau Asabar.

Da yake jawabi yayin taron, shugaban jami’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya yi ikirarin cewa PDP ce za ta lashe zaben gwamnan. Inda ya ce jihar ta PDP ce.

Secondus “Kar ku zabi APC, kar ku bari APC ta murde zaben. Idan APC suka yi murde zaben nan, za su fuskanci fushin jama’a. Abin da Akeredolu yake takama da shi, shine ya murde zabe saboda bai yi kokari ba.

” Ku tabbata kun sauke gwamnatin da ta mayar da jihar Ondo wajen kasuwancin Dangi daya, a sanar da Buhari cewa abu daya da ya rage masa shine gudanar da Sahihin zabe a jihohin Edo da Ondo”.

Shima dan takarar gwamnan jihar na jami’iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya nemi al’ummar jihar su zabi jami’iyyar PDP, inda ya ce idan ya samu nasara a zaben, zai samar da sabon cigaba a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here