Malami Ya Jajantawa Al’ummar da Iftila’in Ambaliyar Ruwa ya shafa a Jihar Kebbi

0
111

Babban Antoni Janar na Kasa kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kebbi bisa iftila’in ambaliyar ruwa da ta yi barna a wasu kananan hukumomi a jihar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai taimakawa ministan kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Dr. Umar Jibril Gwandu ya fitar a yau Asabar 12 ga watan Satumba.

Yayin da yake jaje ga wadanda iftila’in ya shafa, Malami yace gwamnatin tarayya ta na jajantawa ga irin matsin da al’umma suka fada sakamakon ambaliyar ruwa.

Ministan ya tabbatarwa da wadanda lamarin ya shafa cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar yin aiki tare da gwamnatin jiha don samar da kayan tallafi gare su.

Sanarwa ta kara da cewa ministan ya mika sakon jaje ga sarakunan gargajiya na jihar musamman Sarakunan Gwandu, Argungu, Zuru da Yauri bisa rasa mahalli da rayuka sakamakon ambaliyar ruwan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here