Joe Biden Ya na shan Kwayoyin Kara Kuzari kafin ya yi Jawabi gaban Jama’a – Trump

0
140

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yi ikirari ba tare da bada cikakkiyar sheda ba cewa dan takarar shugabancin kasar na jami’iyyar Democratic, Joe Biden yana shan kwayoyin kara kuzari idan zai yi magana a cikin jama’a.

Trump ya fadi hakanne yayin tattaunawa da Fox News.

“Ina tunanin akwai tasirin kwayoyi, haka nima naji”, inji shi.

Trump ya kuma ce ba ya damuwa kan rikici ranar zabe.

” Zamu yi kasakasa da su cikin gaggawa idan suka yi haka”, inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here