Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bukaci Al’ummar Jihar Su Ci gaba da zaman lafiya da Juna

0
154

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya yi amfani da damar walimar da aka shirya don girmama matarsa, Hajiya Silifat Abdullahi Sule da Matar Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu a yau Asabar wajen yin kira ga al’ummar jihar su ci gaba da zaman lafiya tsakanin su.

Gwamnan ya ce saboda samun yanayin zaman lafiya ne har mahalarta taron suka samu damar zama tare don bayyana farin cikin su cikin walwala.

“Yana da matukar muhimmanci ga jama’ar jihar Nasarawa su ci gaba da zama lafiya tsakanin su, su cigaba da girmama dattawan mu, ” Inji gwamnan.

Gwamnan ya godewa Sarkin Lafiya, Justice Sidi Bage mai ritaya, bisa karrama matar sa da ta babban sufeto Janar na ‘yan sanda na kasa.

Injiniya Sule ya bayyana farin cikin sa ga dukkan wadanda suka halarci bikin.

Tun farko a jawabin maraba, tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar Nasarawa, Dr. Zainab Ahmed ta ce an shirya taron ne don girmama matan guda biyu bisa karramawar da sarkin Lafiya yayi musu.

Dr. Zainab ta bayyana cewa adadin yawan matan da suka fito don halartar taron, ya nuna cewa mata a jihar Nasarawa kan su a hade yake kuma kodayaushe za su ci gaba da tafiya a tare.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here