Dabi’ar Lalata da Maza ta Mamaye Masana’antar Shirya Fina-Finai ta Nollywood – Jarumi Maduagwu

0
248

Jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta kasa Nollywood, Uche Maduagwu ya ce dabi’ar auren jinsi ta mamaye masana’antar Nollywood.

Uche ya ce wani jarumi a masana’antar ya yi masa fyade a farkon shirin fim din ya shiga a garin Legas, sannan ya kara da cewa a bani mai matukar wahala ka ga Producer, mai bada umarni ko babban jarumi a masana’antar da baya lalata da jarumai maza.

ya shawarci matasa, da masu shirin zama jarumai da su kiyaye a wajen hada shirin fina-finai(Location), Abinci da abin sha da za a basu a dakin kwana.

Jarumin wanda ya bayyana hakan a shafin sa na Instgram ya ce;

“Maganar gaskiya a duk lokacin da na tuna yadda wani jarumi ya yi lalata dani ya yi min fyade a farkon zuwa na wajen hada shirin fim a Legas, na kan yi kukan bakin ciki.

” Auren jinsi na mamaye masana’antar Nollywood, abu ne mai wuya ka ga mai shirya shiri, mai bada umarni ko babban jarumi wanda baya lalata da wani jarumin musamman idan kai kyakkwawa ne kuma mai kyan fuska.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here