An yi Garkuwa Da Alkalan Kotun Shari’a guda biyu a Jihar Zamfara

0
130

Babban Limamin masallacin Umar Bin Khaddabi dake jihar Zamfara, Shekh Umar Kanoma ya bayyana cewa an yi garkuwa da alkalan kotun shari’a guda biyu a jihar.

Sheikh Umar Kanoma wanda ya yi magana a jiya Juma’a yayin gabatar da huduba ya yi kira ga Al’ummar musulmai da su yi addu’a kan Allah ya kubutar da Alkalan guda biyu.

Limamin ya ce, alkalan guda biyu suna kan hanyar su ta dawowa gida bayan sun halarci taron wa’azi a wajen jihar.

“Mun rokon addu’a daga musulmai da sauran al’umma kan kubutar alkalan kotun shari’a 2 wadanda aka yi garkuwa da su a hanyar su ta dawowa daga Maradi ta kasar Nijar inda suka halarci taron wa’azi”.

Babban limamin ya bayyana sunan alkalan da aka yi garkuwa da su, Mallam Sabiu Abdullahi da Mallan Shafi’i Jangebe.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa daya daga cikin alkalan kotun da aka sace mai suna Mallam Sabiu Abdullahi shine na’ibin limamin masallacin juma’a na Usaimin dake Gusau babban birnin jihar.

Liman Umar Kanoma yayin da yake gabatar da hudubar ya yi kira ga yan bindiga da sauran masu tada zaune tsaye da su tuba su nemi gafarar Allah.

Sannan limamin ya yi kira ga gwamnti a dukkan matakai da su ci gaba da kokarin su na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here