Gobara ta tashi a Ofishin Hukumar INEC na Jihar Ondo

0
134

Gobara ta tashi a ofishin hukumar zabe ta kasa reshen jihar Ondo inda wata majiya ta shedawa jaridar Sahara Reporters cewa gobarar ta lalata Na’urar Card Reader.

Babban jami’in hukumar kashe gobara ta jihar, Mista Adanalwo Philips, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an shawo kan gobarar.

Ya ce “Gobarar ta tashi wajen ajiye kaya ne kawai, wanda yake kusa da ofishin hukumar.

“Ta yadu cikin ofisoshi yayin da muka isa wajen amma mun shawo kan ta”.

An sanya ranar 17 ga watan Oktoba dai a matsayin ranar zaben gwamnan jihar Ondo.

Kuma an sha samun barkewar gobara a ofisoshin gwamnati a yan kwanakin nan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here