‘Duk Masu Goyan Bayan Buhari Makaryata ne Munafukai’ -Shekh Murtala Sokoto

0
398

Shahararren Malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Sokoto, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza, sannan masu goyan bayan Buhari suna fadin ‘Sai Baba’ Makaryata ne kuma Munafukai.

Malamin na fadin hakanne yayin gabatar da lacca ga matasa musulmai.

A wani faifan Bidiyo da jaridar Sahara Reporters ta samu, Malamin yace Buhari bazai iya ziyartar jihar Katsina mahaifar sa ba saboda fushin da al’umma suke dashi.

Ya ce, duk da cewa Buhari ya nada yan Arewa da dama kan mukamai daban-daban, wadanda aka bawa mukamin sun yaudari a al’umma.

Shehin Malamin ya ce “Duk Masu cewa ‘Sai Baba’, makaryta ne, Malalata munafukai. Mutumin da suke kira ‘Sai Baba’ yanzu ba zai iya zuwa jihar Katsina ba. Shi Buhari ya san irin fushin da zai fuskanta idan yaje Katsina.

“Muna addu’a Allah ya taimaki Buhari ya gyara halin sa, a matsayin shugaba, amma idan ya cigaba da yadda yake a yanzu, muna addu’a Allah ya chanza shi da shugaba na gari”.

Malamin ya kara da cewa “Shinkafa, zamu iya ciyar da kan mu? Sun ce mutane su koma gona amma lokacin da kaje gona za’a yi garkuwa da kai. Kai Buhari ka ce muyi noma a Arewa, kaje ka ga Arewa ko’ina. Misali Katsina, ka je Sokoto, Zamfara.

” A wadannan gurare wadanda suke zuwa gona ana garkuwa da su ana neman kudin fansa Miliyan 2 zuwa 3…! Tayaya Manomi a kauye zai samar da miliyan 3, suna cewa muyi hakuri, har zuwa yaushe zamu yi hakurin?.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here