Hukumar Hisbah ta Kama Almajirai 648 a Jihar Kano

0
174

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama Mabarata 648 bisa zargin sabawa dokar hana yin bara a kan titituna.

An kama su ne tun daga watan Fabarairu zuwa yau.

Mai magana da yawun hukumar, Lawan Ibrahim, ne ya fadi hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Kasa(NAN) a yau Laraba.

An kama Mabaratan ne a yankin Baga, Murtala Muhammad Way, Asibitin Nasarawa, Railway satation da mahadar gurin Yahuza Suya.

Ibrahim ya bayyana cewa an kama mata 416 da maza 232 cikin mabaratan.

Hukumar tayi gargadi ga almajirai wadanda suka ki yin biyayya ga dokar hana bara a jihar.

“Zamu tsaftace titunan Kano daga yin bara. Wadanda aka kama an tan-tance su wadanda aka fara kamawa karon farko za’a mika su ga yan’uwan su”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here