Gwamnatin Tarayya ta ce ta biya Miliyan Dubu 20 a matsayin Alawus-Alawus Ga Likitoci

0
114

Karamin Ministan lafiya, Dr. Olurunnimbe Mamora, ya ce gwamnatin tarayya ta biya Biliyan dubu 20 a matsayin allowance na COVID-19 ga Likitoci da ma’aikatan lafiya a kasarnan.

Ministan, wanda ya jinjinawa ma’aikatan lafiya yayin da ake yaki da annobar COVID-19 a kasarnan, ya bayyana hakanne a safiyar yau Laraba yayin shirin gidan talabijin na Channel, mai suna Sunrise Daily.

Kimanin likitoci dubu 16 ne dai suke yajin aiki bisa gazawar gwamnati wajen biyan bukatun su wadanda suka hada da alawus din inshora na cutar COVID-19 da kudin bayar da horo da sauran su.

Likitocin sun kuma nemi a kara yawan alawus din da ake basu na ayyukan na musamman.

“Gwammatin tarayya ba ta gayyace mu tattaunawa ba bayan sanar da su cewa zamu tafi yajin aiki. Mun umarci dukkan manbobin mu dake tarayya da jihohi su fara yajin aikin da muka dakatar a ranar 22 ga watan Yuni,” cewar kungiyar likitoci ta kasa shekaran jiya Litinin.

Sai dai yayin da yake jawabi a yau Laraba ta cikin shirin talabijin na Channel, Minista Mamora ya ce abin takaici ne irin hakan na faruwa a lokacin da kasarnan ke fama da annoba.

Ya ce adadin alawus din dubu 5 da ake bawa likitoci da ma’aikatan lafiya tsawon shekara 30 an dakatar dashi.

Ministan ya ce, “Mun samu damar biyan alawus na COVID-19 saboda mun dakatar da biyan Alawus na lokacin hadari a wannan lokacin don haka zamu shiga tattaunawa bayan hakan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here