Dalilan Da yasa nake Siyar da Man Fetir akan Naira 158 Duk Lita – AA Rano

0
310

Alhaji Auwalu Ali Rano, Shugaban Kamfanin AA Rano, ya ce duk da karin kudin man fetir da aka yi zuwa 162 duk lita, kamfanin sa bazai siyar da mai sama da Naira 160 ba.

Shugaban Kamfanin yayi bayanin hakanne a bude taron bada horo na kwana 6 akan sauyi wajen tafikarwa a Bristol Palace dake Kano yau Laraba.

Ya ce, ya yanke shawarar siyar da man fetir akan Naira 158 zuwa 160 duk lita ne a dukkan gidajen man sa dake fadin Najeriya saboda saukakawa halin matsin da talakawa ke ciki.

Shugaban ya ce kamfanin ya zabi la’akari da halin da Yan Najeriya ke ciki fiye da ribar da zai samu.

“Kamfanin mu a shirye yake a kodayaushe wajen samar da ingantaccen kasuwanci ga yan Najeriya wanda muka dau tsawon shekara 20. Idan zaku iya tunawa koyaushe muna tare da yan kasa a halin matsin da suke ciki”,Inji shi.

Sannan ya bayyana cewa Kamfanin AA Rano ya yi shirin fadada harkokin kasuwancin sa zuw wasu bangarori kamar zirga-Zirgar Jiragen sama da Sauran harkokin kasuwanci.

Haka kuma ya karyata batun cewa kamfanin sa zai kori ma’aikata biyo bayan matsin tattalin arzikin da ake ciki sakamakon annobar COVID-19.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here