Za’a Dena Amfani da Harsunan Yoruba da Igbo nan da Shekaru 50 – NICO

0
178

Babban Sakatare na cibiyar wayar da kai kan al’adu na Kasa, Ado Muhammad Yahuza, ya ce wasu daga cikin harsunan Najeriya da suka hada da Inyamuranci da Yarabanci baza su kai shekaru 50 nan gaba ba indai ba’a dauki matakin gaggawa ba na dawo da amfani dasu yau da kullum.

Muhammad Yahuza ya fadi hakanne a taron shirin wayar da kai kan harsunan Najeriya karo na 2 (NILP) a jiya Litinin a Abuja.

“Akwai alamu da aka nuna kan cewa kashi 90 na harsunan duniya 7,000 suna shirin bacewa a karni mai zuwa, haka lamarin yake a Najeriya.

” Masana sun bayyyana cewa, fiye da rabin harsunan Najeriya 400 suna cikin hatsarin bacewa.

“Karin alamu sun nuna cewa harshen Inyamuranci sa Yarabanci, baza su iya kaiwa shekaru 50 nan gaba ba matukar ba a dauki matakan dawo da amfani da harsunan ba”, Inji shi.

Alhaji Muhammad Yahuza ya ce shirin na NILP da ake yin sa a Bariki na daya daga cikin ayyukan cibiyar wajen wayar da kai kan barazanar bacewar yare tare da bunkasa sha’awar yin amfani da harsunan gida.

“Bariki, kamar yadda duk muka sani gida ne na jami’an tsaro da iyalan sojoji da yan’sanda”, Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here