Muna Kashe Dubu Dari 4 akan Duk Mutum daya Mai Dauke da Cutar Corona -El-Rufai

0
136

Gwamnnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya ce gwamnatin jihar tana kashe Kudi Naira dubu dari 4 kan kowanne mutum daya mai dauke da cutar COVID-19 a Jihar.

El-Rufai ya bayyana hakanne yayin zaman tattaunawa na kwamitin zartarwa tare da Sarakunan gargajiya karkashin jagorancin Sa’ad Abubakar
Sarkin Musulami.

Gwamnan ya ce adadin kudin yayi yawa ne saboda tsadar magunguna, ciyarwa da kuma kayan kariya ga likitoci.

Ya ce, “mun samu babbar nasara a wajen yiwa masu cutar COVID-19 magani. Har dan shekara 90 wanda ke dauke da cutar Siga da hawan jini an masa magani cikin nasara a jihar.

” Cutar bata barmu ba. Zamu iya mantawa da ita, amma tana nan. Muna bukatar ku sanar da mutane su kare kansu daga cutar musamman tsofaffi da suka haura shekara 60.

“Ana kashe kudi Dubu Dari hudu, wajen kula da mai cutar Corona mutum daya. Suna da bukatar a killace su kuma aciyar dasu. Farashin magani ya tashi, har kayan kariya da likitoci ke sawa. Idan ka hada dukkan wadannan kudin zai kama dunu dari 4 duk mutum daya”, cewar Gwamnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here