Farashin Man Fetir a Najeriya Shine Mafi Araha a Afrika – Gwamnatin Tarayya

0
134

Gwamnatin tarayya a jiya Litinin tace duk da karin kudin man fetir da aka yi zuwa 162 duk Lita, farashin man fetir din yana daga cikin mafiya sauki a yankin Afrika.

Ministan yada labarai, Lai Muhammad, ne ya fadi haka a wani taron manema labarai a Abuja.

Lai Mohammed yana tare da ministan wutar lantarki, Sale Mamman da karamin ministan man fetir Timipre Sylva a wajen taron.

Ministan yace “Duk da karin kudin man fetir zuwa 162 duk Lita, farashin man fetir a Najeriya shine mafi sauki a yanki yammaci da tsakiyar Afrika.

“Ga yaddda farashin man fetir yake a wasu kasashen idan aka kwatanta da kudin Naira na Najeriya: Najeriya- 162 duk lita daya, Ghana – 332, Benin -N359, Togo-N300 lita daya, Kamaru-N 449 Lita daya, Kasar Mali ana siyar da Lita daya a Naira 476, Liberia N257 da Senagal inda ake siyar da Lita daya a Naira 549.”

“Yanzu kun gane cewa duk da janye tallafin man fetir, farashin man shine a Najeriya shine mafi sauki a Yankin Afrika”, Inji shi.

Lai Mohammed yace bisa raguwar kudin haraji da kaso 60 gwamnati baza ta iya biyan kudin tallafin man fetir ba.

Inda yayi nuni da cewa tallafin kudin man fetir ya lakume kudi Naira Tiriliyan 10.413 tsakanin shekarar 2006 zuwa 2019.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here