Ganduje Na Son Sarkin Kano Ya Jagoranci Majalisar Sarakunan Jihar Har tsawon Rayuwar sa

0
139

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya nemi majalisar dokokin jihar tayi gyara a dokar masarautu, inda ya nemi a janye batun karba-karba a shugabancin majalisar Sarakunan jihar.

Dokar dai a baya tayi tanadin cewa, wanda gwamna ya nada a matsayin shugaban majalisar Sarakunan zai yi shugabanci na shekara 2.

Sabuwar dokar dai wacce ta wuce karatu na biyu a majalisar dokokin jihar, zata bawa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero damar zama shugaban majalisar Sarakunan na din-din-din.

Yayin zaman majalisar a yau Litinin, shugaban masu rinjaye na majalisar, Kabiru Dashi wanda ya karanta kudurin gyaran dokar, yace kudurin ya kuma nemi a kara yawan masu zabar Sarki a dukkan masarautun jihar.

“A gyaran dokar muna shirin kara yawan masu zabar Sarki a masarautun jihar nan don mayar dasu biyar.

” Saboda muna da masu zabar Sarki mutum 4 a kowacce masarauta, idan aka samu rasuwa ko cire Sarki, muna gudun samun yanayi wanda mutum biyu zasu yarda mutum biyu suki yarda.

“Amma idan su biyar ne, dole a samu gaskiya da gaskiya wajen zabar Sarki. Sannan idan aka amince da dokar zata samar da wa’adin kwanaki 3 domin zabar Sarki”, inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here