Dalibai Yan Asalin Jihar Kano Dubu 10 ne Suka yi Rijista da shirin bada Tallafin Karatu na Schorlarship – Habu PA

0
182

Abubakar Zakari, Babban Sakatare, na hukumar bada tallafin Karatu ta jihar Kano, yace sama dalibai dubu 10 sun nemi shiga tsarin bada tallafin karatu na shekarar 2020 a jihar.

Abubakar Zakari ya fadi hakanne a yau Litinin a Kano yayin ziyarar da daliban da suka kammala jami’ar Al-Mansoura, Egypt suka kai masa.

Inda yace hukumar ta samar da gurbi dubu 40 ga daliban da suka chan-chanta don shiga cikin tsarin a shafinta na Internet. Sannan ya kara da cewa hukumar ta fara rijistar masu son cin gajiyar tallafin karatun a ranar 1 ga watan Satumba.

Babban Sakataren ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta amince a kara yawan kudin da ake bawa daliban jihar da suke karatu a manyan makarantu a kasarnan.

“Gwamnatin jiha ta ware kudi Miliyan 250 don biyan kudin makaranta da sauraran kudade ga daliban mu da suka kammala karatu a jami’ar Al-Mansoura.

“Gwamnatin jiha ta dauki nauyin wasu dalibai a jami’ar amma ba’a biya musu kudin makaranta ba.

“Makarantar ta yanke shawarar dawo dasu gida, bayan haka gwamna Ganduje ya kai musu dauki wanda hakan ya basu damar kammala karatun su, ” Inji shi.

Abubakar Zakari yayi nuni da cewa daliban da suka kammala makarantar tun shekarar 2018, basu samu damar karbar takardar shedar kammala karatun su ba sakamakon rashin biyan kudin makarantar.

Sannan ya kara da cewa hukumar ta samar da hanyar biyan kudin ga jami’ar don bada dama ga daliban su karbi shedar kammala karatun su.

Shima anasa jawabin, Muhammad Yusif, shugaban kungiyar dalibai yan asalin jihar Kano dake Jami’ar Al-Mousura, ya yabawa kokarin hukumar, inda ya kara da cewa abu ne mai fadi wajen taimakawa dalibai su cimma burin su na karatu.

Kungiyar ta kuma gabatar da wasikar yabawa ga babban Sakataren hukumar bisa goyan bayan da yake bawa daliban.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here