Mun Kashe Kudi Sama Da Miliyan Dubu 30 Kan Yaki Da Cutar Corona – Gwamnatin tarayya

0
223

Gwamnatin tarayya tace ta kashe kudi Naira Biliyan 30 a kokarin yaki da cutar COVID-19 tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli na wannan shekarar.

Babban Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris, wanda ya bayyana hakan, yace adadin kudin yayi dai-dai da kaso 84 na Naira Biliyan 36.3 na asusun al’umma da gudunmawa da gwamnatin tarayya ta karba don dakile yaduwar annobar.

Sannan yace Naira Biliyan 5.9 suka rage a yanzu haka.

Ahmed Idris na fadin hakanne a martanin da ya mayar na yancin neman bayanai da kungiyar SERAP tayi.

Daraktan kungiyar ta SERAP, Kolawole Oludare, a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi yace, Akanta Janar din ya bada bayani wanda babu kwanan wata cewa “Kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 ya kashe Naira Biliyan 22; Jihohin Kasarnan 36 sun kashe Naira Biliyan 7 kan yaki da cutar COVID-19″.

Sanarwa ta kara da cewa Ahmed Idris yace” Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe Miliyan 877 wajen kai kayayyaki don yaki da cutar; Rundunar Yan sanda ta kashe Naira Miliyan 500 wajen siyan kayan kariya yayin da aka biya Naira 17, 865.09 a matsayin chaji na banki.

Yayin da take yabawa Ahmed Idris bisa bayar da bayanan, Kungiyar ta SERAP Da ta CODE ta kuma bukace shi ta ya mayar da martani ga sauran bayanan da ake nema cikin wasikar wadanda suka hada da bayyana ayyukan da kwamitin fadar shugaban kasar yayi har suka cinye kudi Naira Biliyan 22 da kuma lissafa yan Najeriyar da suka amfana da aikin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here