Matar Dake Yiwa Maza Aski A Najeriya

0
261

A matsayin ta na Mace a inda Maza suka fi yin jagoranci, Ms Obasi, wacce ta fara sana’ar Aski tun shekarar 2014 tace bata nadamar yin sana’ar tata.

A wata tattaunawa da Jaridar PREMIUM TIMES, ta bayyana alfanu gami da kalubalen kasancewar mace mai sana’ar Aski a Najeriya.

Oyinye ta bayyana cewa bata da sha’awar fara sana’ar Aski, sai dai tana son fara yin sana’a saboda mahaifiyarta ta jaddada mata cewa ta fara sana’a bayan kammala digirin ta na farko.

“Bayan Kammala yiwa kasa hidima, sai naso na koyi sana’a domin faranta ran Mahaifiyata.

” Batun gaskiya shine ban taba ji ko ganin mace tana sana’ar aski ba sai ni dana koya a shekarar 2009.

“Bayan na kammala koyan sana’ar Aski a shekarar 2010, ban samu aiki ba a lokacin, sai na fara sana’ar yin aski kyauta a shagon askin da na koyi sana’ar, har sai dai na samu aiki bayan yin watanni.

” A shekarar 2014, ban samu aiki ba, a wannan lokacin ina yin aiki kyauta ne, naje nayiwa wani mutum aski wanda gashin kansa yake da matsala, na bashi shawara kan irin askin daza ayi masa da gyaran fuskar da zai masa kyau.

“Iya askin da nayi da kuma gyaran fuska shine ya sanya mutumin fada min cewa yasan wani mutum da yake da wajen aski kuma yana neman mai aski mace, sai na bashi lambar waya ta, bayan nan naje aka tan-tance ni sannan na samu aiki a wajen.

“A lokacin na fadawa wanda ya dauke ni aiki cewa zanyi aiki ne a rabin lokaci(Part time) tun da ina yin aikin kyauta a lokacin. A shekarar 2015 sai sana’ar aski ta shiga raina na yanke shawarar kafa wajen sana’a ta mai suna Lush Trends Barbershop a Oregun dake jihar Lagos.” Inji ta.

Mai askin ta kuma kara da cewa lokacin da ta fara sana’ar wasu mazan basu yarda tayi musu aski ba.

Onyinye tace tayiwa shararrun mutane aski a kasarnan” Eh nayiwa Fin Osibanjo, dan mataimakin shugaban kasa aski, Joro Oulumfin, Dayemi Harfysong da sauran shahararrun mawaka na duniya.”

Hakanan Oyinye tayi bayanin cewa wasu matan na ganin baikyanta bisa yiwa mazajen su aski.

“Wani abu da na lura dashi shine, maza suna bada hadin kai ga mai aski, musaman idan sun samu wanda ya iya, to wasu matan baza su taba yarda mace tayiwa mazajen su aski ba”.

Onyinye wacce take da Aure tace mijinta yana bata goyan baya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here