An Umarci Jami’an Tsaro Su Kasance Cikin Shiri Bayan Rahoton Bullar Yan Boko Haram a Abuja

0
122

An sanar da jami’an tsaro a kasarnan su kasance cikin shiri bayan rahoton sirri dake nuni da cewa mayakan Boko Haram na shirin kafa sansani a Babban Birnin tarayya Abuja.

Rahotan yayi bayanin cewa Mayakan tada kayar baya na Boko Haram sun kafa sansanoni a ciki da wajen Abuja, lamarin dake barazana ga lamarin tsaro.

Rahotan na dauke ne cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 4 ga watan Satumba daga babban Jami’in hukumar fasa kwauri ta Najeriya, H.A Sabo a madadin mataimakin jami’in dake kula da sashin bincike

A sakamakon hakan aka umarci dukkan jami’an tsaron kasarnan da su zauna cikin shiri a kowanne lokaci.

Jaridar THISDAY ta rawaito rahotan sirrin na cewa “Rahotanni da dama sun bayyana cewa sun shirin kai hari wasu yankuna a birnin tarayya Abuja.

“Akwai bayanan dake cewa sun kafa sansanin su a wadannn gurare: Dajin Kunyam dake hanyar filin sauka da tashin jirage, Abuja, Dajin Robochi Gwagwalada, Dajin Kwaku Kuje Abuja, Dajin Unaisha dake Karamar hukumar Tata a jihar Nasarawa, dajin Gegu wanda ke kusa da garin Idu na jihar Kogi”.

Sai dai yayin da yake bayyana ra’ayinsa ka batun, Mai taimakawa shugaban kasa kan sha’anin yada labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da cewa hukumar hana fasa kwauri ta samar da wasu bayanan sirri kan sha’anin tsaro.

Gwamnatin shugaban kasa Buhari dai tasha bayyana cewa ta samu nasarar kakkabe kungiyoyin yan ta’adda duk da cewa masu tada kayar bayan na cigaba da kai hari ga jami’an tsaro da al’umma a yankin Arewa maso gabas.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here