‘Zunuban Yan Najeriya ne Ya Jefa Su Halin da Suke Ciki a Yanzu Ba Buhari Ba’ – Magoya Bayan Buhari

0
176

Magoya bayan jami’iyyar APC sun soki masu ganin lafin shugaban Kasa Buhari kan tabarbarewar tattalin Arziki a Kasarnan.

Inda suka ce matsin rayuwa da ake ciki yanzu hukunci ne da Allah yake yiwa yan Najeriya bisa aikata sabonsa da suke yi.

Magoya bayan Buharin a wata waka dake yawo cikin harshen Hausa sun zargi Yan Najeriya da Barin Ubangiji, wanda ya jawo matsin da ake ciki a halin yanzu.

Wakar dai anyi mata suna da “Babu Ruwan Buhari”.

” Mutane yakamta su dena zargin Buhari kan wannan matsalar rayuwa da ake ciki. Zunuban mu ne suka jawo da kon bin umarnin Allah.

“Babu Ruwan Buhari akan wannan abu. Zunuban mu ne suka haifar dashi.

“Mun bar Ubangiji. Don haka Babu Ruwan Buhari.

” Yakamata mu nemi gafarar Allah. Don Babu Ruwan Buhari”, a cewar wakar kamar yadda Jaridar Sahara Reporters ta rawaito.

A yan kwanakin nan dai yan Najeriya nata sukar gwamnatin shugaban kasa Buhari bisa tsadar kayan abinci tare da karin kudin wutar lantarki gami da na man fetir.

Ko dayake shugaba Buhari ya bada umarnin shigo da ton dubu 260 na masara don samar da abincin kaji bayan matsin lamba daga kamfanunuwan hada abincin kajin.

Sai dai wasu na ganin kamata yayi shugaban ya janye dokar hana shigo da kayan abinci kamar su shinkafa mai, da sauran su don magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here