Mutane 4 sun Rasa Ran su yayin da Gidaje 5, 200 Suka Rushe Sakamakon Ambaliyar Ruwa a Kano -SEMA

0
113

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano(SEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 4 da rushewar gidaje 5, 200 sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Rogo da Dambatta.

Sale Jili, Babban Sakataren hukumar ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) a yau Asabar a Kano.

Kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) ya rawaito hukumar kula da yanayi ta kasa  na gargadin samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 20 dake jihar.

Alhaji Jili ya bayyana cewa mutane biyu sun rasa rayukan su yayin da gidaje 200 suka rushe a karamar hukumar Rogo, sannan mutum biyu sun rasu kana gidaje dubu biyar sun rushe sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Dambatta.

“Mun tura tawagar duba abinda ya faru a guraren da abin ya shafa. Haka kuma mun ziyarci Rogo da Dambatta don jajantawa wadanda lamarin ya shafa.

“Akwai rahoton samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 44 dake jihar nan sakamakon samun mamakon ruwan sama a wannan lokaci”, inji shi.

Babban Sakataren hukumar yace mutanen da suka rasa gidajen su yanzu haka sun koma gidajen yan’uwan su a yankunan da abun ya shafa.

Jili,  ya kuma ce hukumar ta raba kayan tallafi da kudin su yakai Naira Miliyan 3 da Dubu dari biyar ga wadanda abin ya shafa don rage musu radadin abin.

Ya zayyana abubuwan da hukumar ta rarraba da suka hada da Buhun Siminti, Kayan abinci, abun rufe daki, tabarmi da sauran su.

Sannan ya shawarci mazauna Kano su kwashe shara a mugudanun ruwa kuma su kauracewa zama a hanyoyin ruwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here