Jami’iyyar APC na Bukatar Kudi Daga Ma’aikatar Man Fetir Don yin Yakin Neman Zabe – Gwamnan Ondo

0
176

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, yace jami’iyyar APC tana bukatar Kudi daga Ma’aikatar Albarkatun mai don yin amfani dasu wajen samun nasarar zaben gwamnan jihar da za’a gudanar.

Akeredoli ya bayyana hakan ne a garin Akure a yau Asabar yayin gangamin yakin neman zabensa karo na 2.

Gwamman yace, “Ina yiwa kowanne minista barka da zuwa, Abokina Sylva yana nan wajen, muna bukatar kudi. Shine ministan man fetir kuma dole ya bayar”.

Haka kuma, jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da ofishin tattara haraji na jihar Ondo dake titin Igbatoro a garin Akure.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here