Darajar Naira za ta ci gaba da faduwa Matukar Najeriya ba ta rage yawon shigo da kayayyaki daga Kasashen Ketare ba – Sanusi

0
167

Muhammadu Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya(CBN), Yace darajar Naira za ta ci gaba da faduwa har sai Najeriya ta rage shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.

Babban bankin Najeriya dai ya karya darajar Naira har sau biyu a wannan shekarar ta 2020; da farko daga N306 a matsayin Dala daya zuwa 360 a maimakon Dala daya sannan an kara karya darajar Naira daga 360 a matsayin dala daya zuwa 380 a matsayin dalar Amuruka daya.

Sanusi yayin da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Arise yace kasarnan na shigo da kayan da za’a iya yin su a cikin gida da wadanda baza a iya yin su a gida ba.

Tsohon Sarkin Kanon ya kuma soki dogaron da gwamnati tayi akan man fetir kadai, inda yace irin haka ne ya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin wani hali.

Sanusi yayi bayanin cewa Darajar Naira zata karu idan Najeriya ta hada kai da kasashen yammacin Afrika.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here