Anyi Jana’izar Zainabu Abubakar Yar’uwa Ga Sarkin Karaye

0
249

Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar Hajiya Zainabu Abubakar II ,Yar’uwa ga Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II.

Alhaji Dr. Abubakar II shine Sarkin Karaye a jihar Kano.

Haruna Gunduwa, Jami’in yada labarai na masarautar Karaye ya tabbatarwa da Jaridar PRIME TIME NEWS labarin a wata sanarwa da ya aiko mata.

Imam Kabiru Hassan Karaye ne ya jogaranci yi mata sallar jana’iza a fadar Sarkin Karaye da misalin Karfe 9.07 na safe.

Jana’izar ta samu halartar Sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II, Shugaban karamar hukumar Karaye, hakimai da sauran manyan mutane daga ciki da wajen masarautar.

Marigayi Hajiya Zainabu Abubakar ta rasu ne a yammacin jiya bayan gajeriyar rashin lafiya, ta rasu ta bar dan’uwanta Sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II.

An binne gawarta a makabartar Burga dake garin Karaye.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here