‘Zan Gina tattalin Arzikin Karni na 20 Idan na Zama Shugaban Najeriya’ – Orji Kalu

0
126

Babban mai tsawatarwa na majalisar dattijai kuma mai neman takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Orji Uzur-Kalu, yace idan yan Najeriya suka bashi damar zama shugaba kasa, zai gina tattalin arziki na karni 20.

Yayin da yake magana a wani shirin gidan Rediyo a garin Umuhahi wanda jaridar The Sun ta saurara, Mista Uzor-Kalu yace ya shirya yin aiki.

“Eh, Idan kuka bani damar zama shugaban kasa, zan karba, na shirya yin aiki”, inji shi.

“Matsalar shine waye zai iya yin aiki. A yanzu na mayar da hankali wajen aikin mazabata; akwai aiki dayawa daza’a kammala.

“Idan kuka bani dama, zan so na koma majalisar dattijai a karo na biyu, amma idan yan Najeriya suna so na zama shugaban kasa, zasu ga kwarewata.

” Zan yi aiki. Zan gina tattalin arziki na karni 20 ga mutanen mu”,Inji ni.

Mista Orji Kalu ya fara tuntuba a makon da yagabata yayin da ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar a garin Minna na jihar Naija.

Yayin ziyarar, Mista Uzor-Kalu ya bayyana cewa idan masu zabe suka bashi dama zai yi shugabanci nagari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here