Yan Sanda a Kano Sun ceto Saurayin da Yaso Kashe Kan sa Bayan Ya Gaza Samun Auren Yar Shugaban Kasa Buhari

0
666

Daukin gaggawa da jami’an yan sanda suka kai a yau juma’a ya ceto Abba Ahmed daga kashe kansa bayan ya rasa soyayyar sa ga yar shugaban kasa Muhammadu Buhari Hanan Buhari

Kwararrun jami’an yan sanda sun ceto Abba Ahmed mai shekaru 22, dan ajin karshe a sashin ilimin ajiyar kudi na jami’ar Yusif Maitama Sule, Kano bayan bashi shawarwari wanda yasa Abba ya chanza shawara.

Sannan yana kasuwancin siyar da kayan sawa a kasuwar Kantin Kwari.

Abba yace yanzu a shirye yake ya fara sabuwar rayuwa tare da wacce take son sa.

An daura Auren Hanan Buhari dai a yau Juma’a da Angon ta Turad Sha’aban, Da ga Damburan din  Zazzau a wani karamin biki da aka gudanar.

A kwanakin baya ne dai Abba ya wallafa a shafinsa na twitter cewa zai kashe kansa matukar bai samu auren Hanan ba.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda na kasa, Mista Frank Mba bayan yaduwar rubutun na Abba, ya sanar da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Habu Sani don gayyato Abba wanda yake zaune a Kano.

Frank Mba yayi magana da Abba ta wayar tarho tsawon minitina 7, inda ya shawarce shi da ya mayar da hankali wajen cigaban rayuwarsa maimakon ya halaka kansa.

Abba, wanda yayi nadamar yunkurin da yayi na kashe kansa bayan karbar shawara daga rundunar ‘yan sandan, sannan ya nuna sha’awar sa ta shiga aikin dan sanda.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here