Matasa Na Zanga-Zanga a Jihar Osun Kan Karin Farashin Man Fetir

0
118

Matasa sun yi dandazo a kan tititunan garin Osogbo, babban birnin jihar Osun inda suke zanga-zanga bisa karin kudin man fetir da na wutar lantarki.

Gwammatin tarayya dai, a ranar Laraba ta hanyar kamfanin kula da farashin man fetir(PPMC) ta kara farashin man daga 138 zuwa 151.56 kowacce Lita, wanda ya bawa yan kasuwa damar kara kudin litar man zuwa 162.

Masu zanga-zangar sun taru a Nelson Mandela Freedom Park, inda suka nufi mahadar Ola-Iya da misalin karfe 9:15 na safe.

Matasan suna rike da kwalaye a hannun su wadanda aka yi rubutu maban-banta.

Masu zanga-zangar sun bawa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 5 ta janye batun karin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here