Kungiyar Dalibai ta Kasa ta Nemi Shugaba Buhari yayi Murabus

0
173

Kungiyar Dalibai ta kasa shiyya ta uku( NAN Zone D), taki amincewa da sabon farashin litar man fetir na Naira 148 zuwa 151 da gwamnatin tarayya ta sanar.

Shugaban kungiyar Daliban ta NANS (Zone D), Kowe Odunayo Amos, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ya bayyana karin kudin man fetir a matsayin hukunta yan Najeriya ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa sakamakon bullar annobar Corona.

Kungiyar Daliban ta nemi shugaba Buhari ya janye karin kudin man fetir din ko yayi murabus.

Sanarwar tace,”Babu tantama, wannan gwamnatin ta kara munana dukkan wata matsala da ta gada daga tsohuwar gwamnati. A takaice ma, Gwamnatin Buhari misali ne mai kyau cewa mu dalibai dole mu koma yan juyin juya hali.”

“A matsayin mu na Kungiyar Dalibai, muna sanar da cewa gwammatin Buhari dole ta sauka ko ta dawowa da farashin man fetir zuwa 97 sannan ta dena kaskantar da fannin man fetir, ta dena rage darajar Naira. Sannan dole ta kara kashi 35 ga fannin iilimi a kasafin kudi. Ini sanarwar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here