Karin Kudin Wutar Lantarki Ya Fara Aiki a Jihohin Kano, Jigawa da Katsina -KEDCO

0
303

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kano(KEDCO), yace ya fara aiwatar da karin kudin wutar lantarki da hukumar kula da hasken wutar lantarki ta amince dashi.

A wata sanarwa da aka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS a yau Alhamis daga babban jami’in yada labarai na kamfanin, Ibrahim Sani Shawai tace karin kudin wutar lantarkin zai fara aiki ga masu hulda da kamfanin wadanda basu da Mita daga ranar 1 ga watan Satumba da muke ciki.

Sanarwar tace, tsarin zai bunkasa samar da wuta ga yan kasuwa da magidanta a kokarin kamfanin KEDCO na bunkasa samar da nagartaccen aiki ga masu hulda dashi a jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

Sanarwa ta kara da cewa, sabon karin kudin wutar zai kasance ne akan tsarin yadda aka samar da wuta da kuma lokacin samar da ita. Don haka masu amfani da wutar lantarki zasu biya kudin wuta dai-dai awannin da suka sha. A sabon tsarin biyan kudin wutar an rarraba masu amfani da wutar zuwa kashi 5 A, B, C, D da E.

Masu amfani da wutar lantarki a rukuni na A zasu samu wutar awa 20 yayin da na rukunin B zasu samu wutar lantarki mafi karanci ta awa 16. Yan rukunin C zasu samu ta awa 12 sannan yan rukunin D da E zasu more wutar Awa 4 zuwa 8.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here