Hukumar Dake Kula da Jami’o’i ta Kasa NUC ta Gamsu da Gine-Ginen Jami’ar Maryam Abacha dake Kano

0
242

Hukumar dake kula da jami’i’o ta kasa , NUC ta gamsu da gine-ginen dake a jami’ar Maryam Abacha American University da aka kafa a Kano.

Daraktan kula da sha’anin jama’a na hukumar NUC, Ibrahim Yakasai, ne ya bayyana gamsuwar a yau Alhamis, jim kadan bayan gudanar da zagayen duba gine-gine a matugunin jami’ar dake Hotoro cikin Birnin Kano da Garin Gwarzo na jihar Kano.

Alhaji Yakasai yace “Kamar yadda kuka sani yayin da jami’ar da ake shirin kafawa ta nemi sahalewa, muna ziyarta jami’ar domin duba gine-gine da sauran gurare don tabbatar da cewa ta shirya fara karatu, toh abinda muka gani anan abin gamsuwa ne”.

Yayin da yake karfafa gwiwar kafa karin jami’i’o masu zaman kansu, Daraktan ya bayyana cewa adadin jami’i’on da ake dasu masu zaman kansu dana gwamnati, sun yi kadan wajen daukar adadin daliban dake neman gurbin karatu duk shekara.

Sannan yace kafa karin jami’i’o a kasarnan zai baiwa yan kasa dama wajen samun ilimi mai inganci.

” Akwai sama da masu zana jarrabawa Miliyan 2 da suke kokarin samun gurbin karatu a manyan makarantun kasarnan duk shekara yayin da damar da makarantu 177 suke dasu bai gaza daukar dalibai dubu dari 5 ba, don haka akwai bukatar kafa karin manyan makatantu a kasarnan”. Inji shi.

Shima anasa jawabin tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, ya jinjinawa wanda ya kafa jami’ar, farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.

Inda yace mutanen Kano yakamata su godewa Allah bisa yadda ya azurta jihar da Abubakar Gwarzo wanda ya bayyana shi a matsayin mai kishin jihar Kano.

“Shekaru biyar da suka gabata, ban taba tunanin wani daga wanan yankin zai zuba hannun jari a harkar ilimi ba kamar yadda wannan matashin dattijon yayi.

” Duba jihar Ogun, a yadda take yar karama tana da jami’o’i masu zaman kansu guda 18. Don haka yakamata muyi maganin kalubalen dake gaban mu don cimma gaci”, Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here