Gwamnatin Tarayya ta bada Umarnin Sake Bude Sansanin Masu Yiwa Kasa Hidima

0
145

Gwamnatin tarayya ta bada dama ga hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta NYSC ta fara shirin sake bude sansanin yan yiwa kasa hidima a fadin kasarnan.

A watan Maris ne dai aka rufe sansanin yan yiwa kasa hidima a matakan da ake dauka na dakile yaduwar cutar Corona.

Babban Jami’in dake kula da tsare-tsare na kwamitin karta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19, Dr. Sani Aliyu yace “Dangane da hukumar NYSC, hukumar kula da masu yiwa kasa hidimar zata fara shirin bude sansanin masu yiwa kasa hidima bisa matakan da aka sanya.

“Muna kan aikin samar da matakai don tabbatar da cewa ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba yayin da ake bude sansanonin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here